Isa ga babban shafi

Birtaniya: Ma'aikatan layin dogo na yajin aiki saboda tsadar rayuwa

Kungiyar ma’aikatan sufurin jiragen kasar Birtaniya ta tsunduma yajin aiki mafi girma da kasar ta taba fuskanta cikin sama da shekaru talatin, saboda bukatar karin albashi sakamakon hauhawan farashin kayayyaki da mukamashi.

Fasinjoji na jiran jirgin kasa a wata tasha dake birnin Landan na Birtaniya a 2010.
Fasinjoji na jiran jirgin kasa a wata tasha dake birnin Landan na Birtaniya a 2010. REUTERS/ Paul Hackett
Talla

Kungiyar ma’aikatan jiragen kasa na Birtaniyta RMT ta ce fiye da ma'aikata 50,000 za su shiga yajin aikin kasa baki daya na tsawon kwanaki uku, wanda ke zuwa adaidai lokacin da aka shirin manyan bukukuwa masu farin jini, da suka hada da bikin kade-kade na Glastonbury.

Makarantu

Makarantun Birtaniya dai na gargadin cewa yajin aikin zai shafi yara da yanzu haka ke rubuta babbar jarabawa.

To sai dai kungiyar RMT tace yajin aikin ya zama dole saboda yadda albashin ma’aitaka ya gaza tafiya daidai da hauhawar farashin kayayyaki, ta yadda ya ba’a taba gani ba cikin shekaru 40.

Sufurin jiragen sama

A hakin da ake ciki filin tashi da saukar jiragen sama na Brussels ya soke tashin jiragen dake fita, bayan da akasarin jami'an tsaron filin  suka shiga yajin aikin, na neman karin albashi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.