Birtaniya zata mika shugaban WikiLeaks Assange ga Amurka
Shafin kwarmata bayanan sirri na WikiLeaks ya caccaki gwamnatin Birtaniya kan matakinta na amincewa da mika shugabansa Julian Assange ga Amurka, inda shafin ya sha alwashin daukaka kara kan matakin.
Wallafawa ranar:
Cikin sanarwar da ya fitar, shafin na WikiLeaks ya bayyana wannan rana a matsayin mai cike da duhu ga 'yancin 'yan jarida da kuma dimokaradiyyar Burtaniya.
Shafin kwarmata bayanan ya kuma nanata cewar Assange, mai shekaru 50, "bai aikata wani laifi ba sabanin tuhumar da ake masa, da kuma azabtar da shi saboda kawai ya yi aikinsa.
Tuni dai magoya bayan Julian Assange suka sha alwashin dakile tasa keyarsa zuwa Amurka da Birtaniya ke shirin yi, domin fuskantar shari’a kan buga bayanan sirri na soja.
Amurka na son gurfanar da Assange a gaban kuliya bisa laifin karya dokar leƙen asiri ta hanyar buga bayanan sojanta da na diflomasiyya a shekara ta 2010, inda zai iya fuskantar ɗaurin shekaru 175 a gidan yari idan aka tabbatar da laifin da ake tuhumarsa da aikatawa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu