Isa ga babban shafi

Faransa za ta yaki tsananin zafi ta hanyar dashen ciyawa

Gwamnatin Faransa ta ware Yuro miliyan 500 don bunkasa ayyukan dashen ciyawa a birane saboda magance tsananin zafi a kasar, yayin da aka fara fuskantar tsananin zafi a kudancin kasar.

Yadda jama'a ke shakatawa a wani dandali mai cike da ciyayi da danshi.
Yadda jama'a ke shakatawa a wani dandali mai cike da ciyayi da danshi. AFP
Talla

Gwamnatin Faransar ta ce wannan wani mataki ne na samar da wurare masu danshi a unguwannin biranen kasar, ta hanyar bada tallafin ga dai-daikun mutane da kuma mahukuntan kananan hukumomi domin karfafa masu gwiwa wajen yaki da sauyin yanayi.

Kakakin gwamnatin kasar Olivia Gregoire ta shaida wa manema labarai cewa, domin cimma wannan buri, gwamnati ta ware kudi har Yuro miliyan 500 domin bunkasa shirin.

Jami’ar,  ta yi kira ga Faransawa su yi taka tsan-tsan yayin da yanayin zafi ke kara ta’azzara a kudanci da kuma kudu maso yammacin kasar.

Masana yanayi sunyi hasashen za’a fuskanaci tsanin zafi wanda zai haura sama da maki 40 a ma'aunin Celsius tsakanin ranakun Alhamis zuwa Asabar a kudancin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.