Isa ga babban shafi

Burtaniya na shan matsin lamba kan mutanen da aka yenkawa hukuncin kisa a Ukraine

Gwamnatin Birtaniya na fuskantar matsin lamba don ganin ta ceto ‘yan kasarta biyu da wani dan Moroco daya da wata kotu mai goyon bayan Rasha a Ukraine ta yankewa hukuncin kisa.

Wasu 'yan Burtaniya biyu Aiden Aslin, da Shaun Pinner, da kuma dan kasar Morocco Saaudun Brahim, a tsakiya, suna tsare a hannun dakrun dake goyon bayan Rasha a Ukraine.
Wasu 'yan Burtaniya biyu Aiden Aslin, da Shaun Pinner, da kuma dan kasar Morocco Saaudun Brahim, a tsakiya, suna tsare a hannun dakrun dake goyon bayan Rasha a Ukraine. AP
Talla

Kotun dake Donetsk, daya daga cikin yankunan biyu na gabashin Ukraine da suka ayyana zaman kansu, ta zartar da hukuncin kisa ga mutanen uku bayan da sojojin Rasha suka kama su.

Brahim Saadoun tare da 'yan kasar Birtaniya Aiden Aslin da Shaun Pinner an ce sun mika wuya ga dakarun Rasha a watan Afrilu bayan sun taimakawa sojojin Ukraine fafatawa a birnin Mariupol mai tashar jiragen ruwa.

Sojojin haya

Hakan na zuwa ne yayin da wani shugaban 'yan awaren da ke goyon bayan Rasha a gabashin Ukraine ke cewa ba zai sauya hukuncin kisa da aka yanke wa 'yan Birtaniyya da wani dan kasar Moroko din ba.

Denis Pushilin, shugaban 'yan awaren yankin Donetsk, Yace "Sun zo Ukraine ne domin kashe fararen hula saboda kudi, shi ya sa ban ga wani sharadi na sassautawa ko sauya hukuncin ba,"

Pushilin ya ce iya adalci kenan da kotun ta yi ga mayakan uku.

Ministan majalisar ministocin Birtaniyya Brandon Lewis ya shaida wa Sky News cewa gwamnati na tattaunanawa da hukumomin Ukraine wajen kokarin taimakawa Aslin da Pinner samun ‘yanci daga hukunci na abin kunya".

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.