Hungary ta hana a bai wa Ukraine makamai
Kasar Hungary ba za ta bai wa kasashen duniya damar kai wa Ukraine makaman da za ta yaki Rasha da su ta sararin samaniyarta ba, bayan da kungiyar kasashen Turai tace zata aikewa kasar makaman yaki.
Wallafawa ranar:
Ministan Harkokin Wajen kasar Peter Szijjarto ya bayyana haka, inda yake cewa ba za su bari ayi amfani da sararin kasarsu wajen aikewa da makaman masu hadari ba.
Ministan ya ce, sun dauki wannan mataki ne domin kare lafiyar jama’ar kasar su dake gida da kuma wadanda ke zama a cikin kasar Ukraine.
Szijjarto ya ce ana iya amfani da safarar makaman wajen kai harin soji wanda ke iya yiwa jama’ar su illa.
Ministan ya ce babban abin da ke gabansu a wannan lokaci shi ne tabbatar da lafiyar kasarsu da kuma jama’arta, saboda haka ba zasu saka hannu a yakin dake gudana a makociyar su ba.
Babban jami’in diflomasiyar kasashen Turai Josep Borrell ya ce zasu bada Euro miliyan 450 domin sayawa Ukraine makaman yakin da za’a mika mata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu