Isa ga babban shafi
Faransa

Macron na shirin neman wa'adi na biyu a zaben Faransa

Yayin da ake jira nan da wani dan lokaci shugaban Faransa Emmanuel Macron ya gabatar da anniyarsa ta sake takara a zaben watan Afrilu da ke tafe, bayanai na cewa shugaban zai gudanar da gangamin neman tazarcensa na farko a ranar 5 ga watan Maris a birnin Marseille.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron AP - Ian Langsdon
Talla

A cewar wasu majiyoyi daga jam’iyyar LREM mai mulkin kasar, shugaba Emmanuel Macron zai gabatar da anniyar takararsa ce wani lokaci cikin mako mai kamawa kafin cikar wa’adin ranar 4 ga watan Maris.

Kafin wannan lokaci dai shugaba Macron ya nisanta kansa daga duk wani batu da ya shafi shirye-shiryen tinkarar zagayen farko na zaben da zai gudana a ranar 10 ga watan Afilu dake tafe, inda ya maida hankalinsa kacokan ba dare ba rana wajen kokarin diflomasiyya na dakile rikicin Rasha da Ukraine, kai kace baida ma bukatar neman tazarcen.

 ‘Yan adawar dai na zarginsa da “labewa” karkashin inuwar shugabancin kasa yana gudanar da yakin neman zabe, la’akari da ziyarce -ziyarce da yake da kuma taruka a wasu yankunan kasar.

Akasarin Kuri'o’in jin ra'ayin jama'a da aka gudanar sun nuna cewa akwai yiyuwar Macron ya lashe zagayen farko na zaben a ranar 10 ga watan Afrilu mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.