Macron ya sha alwashin aiki da Hungary a jagorancin wucin gadin Faransa a EU
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya bayyana gamsuwa da shirin aiki tare da Firaministan Hungary Viktor Orban lokacin da kasar za ta karbi ragamar jagorancin Turai a watan Janairu.
Wallafawa ranar:
Yayin ziyarar Budapest wadda ita ce irinta ta farko da wani shugaban Faransa ya kai tun daga shekarar 2007, shugaba Emmanuel Macron ya bayyana gamsuwar sa da tattaunawar da suka yi da Viktor Orban da zummar yin aiki tare domin gina Turai.
Macron ya ce su na da banbance banbance a tsakanin su, amma kuma suna da aniyar aiki tare saboda nahiyar Turai da kuma zama masu amana a tsakaninsu.
Orban wanda Macron a makon jiya ya bayyana shi a matsayin abokin adawar siyasa, amma kuma abokin tafiya a Turai, ya ce ya amince da shirin yin aiki tare da shugaban na Faransa.
Orban ya ce tabbas sun fahimci juna akan abubuwa guda 3 da suka hada da son kasashensu da bukatar yiwa Turai aiki da kuma bukatar ‘yancin kasashen Turai.
Firaministan ya ce inda su ke da matsala ita ce batun tsaron Turai da makamashin nukiliya da kuma harkar noma.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu