Isa ga babban shafi
Turai-Sufuri

EU ta haramta jiragen sama 97 keta samaniyarta

Hukumar Tarayyar Turai ta sabunta bakin-kundin sunayen jiragen sama da ta haramta musu keta sararin samaniyar nahiyar saboda yadda suke karya dokokin kariya na kasa da kasa.

EU ta haramta jiragen sama 97 keta sararin samaniyarta saboda karya doka
EU ta haramta jiragen sama 97 keta sararin samaniyarta saboda karya doka AP - Jonathan Hayward
Talla

 

Yanzu haka bakin-kundin na kunshe da sunayen kamfanonin jiragen sama 97 da Hukumomin Turai suka haramta musu keta sararin samaniyar nahiyar, adadin da ya yi kasa daga 103 da a can baya wannan doka ke aiki a kansu.

An samu raguwar adadin ne daga 103 zuwa 97 biyo bayan cire sunayen jiragen Moldova da dama daga cikin baki-kundin sakamakon gyatta tsarinsu na samar da kariyar fasinjoji a kasar.

Wannan bakin-kundi na kunshe da sunayen daukacin kamfanonin jiragen saman a wasu kasashen duniya 15 da suka hada da Afghanistan da Angola da Armenia da Congo da Jamhuriyar Demokuradiyar Congo da Djibouti da Equitorial Guinea da Eritrea da Kyrgystan da Liberia da Libya da Nepal da Sao Tome and Principe da Saliyo da kuma Sudan.

Kazalika akwai dai-daikun kamfanoni da matakin ya shafa kamar Med-View na Najeriya da Air Zimbabwe da Skol Airlines na Rasha da Iraqi Airways da Aseman na Iran da Avior Airlines na Venezuela.

Sanarwar da Hukumar EU ta fitar ta ce, an dauki matakin haramta wadannan jirage ne saboda yadda hukumomin kasashensu ke sakacin kula da lafiyar fasinjoji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.