Isa ga babban shafi
Turkiya

Shugaban Turkiyya ya janye barazanar korar jakadun kasashe 10

Shugaban Turkiyya Recep Tayyib Erdogan ya janye barazanar sa na korar wasu jakadun kasashen Turai 10 sakamakon zargin su da matsawa gwamnatin sa lamba na sakin wani dan gwagwarmaya da gwamnatin ta kama.

Recep Tayyip Erdogan, shugaban Turkiyya.
Recep Tayyip Erdogan, shugaban Turkiyya. Osvaldo Silva AFP/File
Talla

Tun a Litinin din makon jiya ne Erdogan ya yi barzanar sallamar jakadun kasashen Canada, Denmark, France, Germany, Netherlands Norway Sweden Finland, Newzealnad da Amurka, bisa zargin su da hada baki wajen yi wa kasar zagon kasa.

Duk da cewa ana ganin Erdogan ya yi amai ya lashe kan batun sallamar jakadun, ba kuma tare da ya bada wasu hujjoji ba, ya gargade su da su yi taka tsan-tsan.

Kafin Erdogan ya bada sanarwar sai da majalisar zartaswar kasar ta tattauna batun sallamar jakadun, inda ta ce kai tsaye suna katsalandan ne ga zaman lafiya da kuma tsare-tsaren kasar.

Kasar ta Turkiyya wadda mamba ce a kungiyar tsaro ta NATO ta jima tana samun rashin jituwa da kasashen turai, saboda banbancin ra’ayi irin na siyasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.