Isa ga babban shafi
fARANSA - SIYASA

Hidalgo na bukatar ganin an fara anfani da kekuna zalla a birnin Paris

Guda daga cikin ‘yan takarar shugabancin kasar Faransa Anne Hidalgo na yunkurin ganin an koma amfani da kekuna zalla a birnin Paris nan da shekaru biyar a wani bangare na gudunmowar Faransa wajen yaki da dumamar yanayi da gurbatar muhalli.

Magajiyar garin birnin Paris kuma 'yar takarar neman shugabancin Faransa a jam'iyyar Socialist Anne Hidalgo, 12/09/21.
Magajiyar garin birnin Paris kuma 'yar takarar neman shugabancin Faransa a jam'iyyar Socialist Anne Hidalgo, 12/09/21. AFP - THOMAS SAMSON
Talla

‘Yar takarar ta shugabancin kasar Faransan karkashin jam’iyyar ‘yan gurguzu tace matukar aka narka Yuro miliyan 250 za’a iya cimma wannan muradi cikin sauki.

A cewar Anne Hidalgo mayar da Paris birnin da ake amfani da keke zalla zai taimaka kwarai wajen kare muhalli da kuma tattala tattalin arziki.

Wannan kuduri na Anne Hidalgo tuni ya fara samun goyon baya musamman ga mazauna biranen da ake samun yawan ababen hawa ba wai iya Paris ba.

A cewar ta duk shekarar gwamnatin Faransa na narka biliyoyin Yuro wajen tallafawa kamfanonin samar da motoci na cikin gida da kuma shigar da wasu kasar wanda ta dage kan cewa komawa amfani da keke zai rage yawan kashe wadannan kudade.

Anne Hidalgo ta ci gaba da cewa a binciken da ta gudanar da ta gano cewa Yuro miliyan 180 zai isa wajen samar da kyakyawan tsarin fara amfani da kekunan a birnin na Paris ciki kuwa har da samar da hanyar da mahaya kekunan zasu rika bi a manyan tituna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.