Isa ga babban shafi
Faransa-Amurka

Macron ya gana da Blinken don gyara dangankatar Faransa da Amurka

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya gana da sakataren harkokin wajen Amurka Antonio Blinken karon farko tun bayan da rashin jituwa ta shiga tsakanin kasashen biyu kan batun cinikin jirgin ruwan yaki na karkashin teku da Faransan ta kulla da Asutarlia.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. REUTERS - POOL
Talla

Tattaunawar Shugabannin biyu da suka kwashe tsawon mintuna 40 suna yi, ta mayar da hankali ne kan yadda kyakyawar dangantakar su zata dai-daita tun bayan da Faransa ta zargin Amurka da cin dunduniyar ta.     

Tuni dai Faransa ta ce tana nan kan matsayar ta na cewa a yanzu ba zata sake sakin jiki da Amurka da Asutarlia ba, saboda yadda a cewar ta suka yaudare ta, kuma za’a sha jan aiki kafin dangantakarsu ta koma dai-dai.

Cacar baka da shan alawashi tsakanin Faransa da Amurka ta kunno kai tun bayan da Faransa ta zargi Amurka da yi maka zagon kasan da ya yi sanadiyyar kwace cinikin da Austarlia ta kulla da ita tare da mayar da shi hannun Amurkan.

Jim kadan bayan hakan ne kuma Faransan ta janye jakadun ta daga Amurkan da Austarlia tare da shan alwashin daukar mataki kan Amurka, wanda kuma ta fara da janye jakadun ta daga kasashen biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.