Isa ga babban shafi
EU-Birtaniya

EU ta raba wa mambobinta kudin tallafin Brexit

Gwamnatocin kasashen Turai sun amince da Euro biliyan 5 da miliyan 400 a matsayin kudaden tallafin gaggawa ga mambobin kasashen Turai da ficewar Birtaniya daga EU ta wujijjiga tattalin arzikinsu.

Wakilan EU da Birtaniya
Wakilan EU da Birtaniya AP - Eddie Mulholland
Talla

Daga karshe dai, gwamnatocin kasashen na Turai sun amince da lale makudaden kudaden tallafin, inda za a mika  kaso mafi tsoka ga Ireland da Faransa.

Ireland wadda ita ce kasa daya tilo da ta raba iyakar kan tudu da Birtaniya a Turai, za ta amshi Euro  biliyan 1 da miliyan 100 daga kudin domin gyagijewa daga koma-bayan tattalin arzikin da ta fuskanta saboda raba gari da Birtaniya.

Ita kuwa Faransa za ta samu Euro miliyan 735, inda za a zuba kaso mafi girma ga bangaren harkar Su, lura da cewa, wannan bangaren ya samu tawaya sakamakon karancin damar shiga cikin Kogin Birtaniya a yanzu.

A ranar 24 ga watan Disambar bara ne, gwamnatin Birtaniya da mahukuntan Brussels suka cimma matsaya cikin kurarren lokaci kan yarjejeniyar kasuwanci tsakanin bangarorin biyu bayan sun raba gari.

Yarjejeniyar ta kunshi safarar wasu kayayyakin masarufi tsakananin bangarorin biyu ba tare da biyan kudaden haraji ba.

Ita ma dai Birtaniya ta bullo da wani shiri na dadada wa al’ummarta da ka iya fuskantar radadin wanann rabuwa da ta yi da EU.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.