Adadin mutanen da suka mutu a girgizar kasar Haiti ya zarce 700
Ma'aikatan agaji sun dukufa wajen kokarin ceto wadanda suka tsira da rayukansu, da kuma gawarwakin mutanen da suka mutu daga karkashin baruguzan gini a Haiti, bayan da girgizar kasa mai karfin maki 7.2 ta afkawa kudu masu yammacin kasar da safiyar jiya Asabar.
Wallafawa ranar:
Kawo yanzu mutane 724 aka tabbatar da mutuwarsu a girgizar kasar da ta rusa dubban gine-gine a kasar ta Haiti, wadda har yanzu ba ta kammala murmurewa daga mummunar girgizar kasar shekarar 2010 ba.
Ma’aikatar binciken karkashin kasa ta Amurka ta ce, inda girgizar kasar ta auku na da nisan kilomita kimanin 160 daga tsakiyar Port-au-Prince babban birnin kasar Haiti da ke da cinkoson jama'a.
Hotunan da aka yada a kafofin intanet sun nuna yadda aka ji girgizar kasar da ta shafe tsawon lokaci tana wanzuwa a mafi akasarin yankunan Caribbean, wadda ta rushe dubban makarantu da gidaje a yankin kudu maso yammacin Haiti.
Hukumar kare fararen hula ta kasar ta ce awanni bayan girgizar kasar adadin wadanda suka mutu na ci gaba da karuwa, inda daruruwan mutane sun jikkata, wasu kuma sun bace.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu