Isa ga babban shafi
Sama jannati

Jirgin attajiri Branson ya kafa tarihin balaguro zuwa saman jannati

Burin attajirin Birtaniyar nan, Richard Branson ya cika a ranar Lahadi, inda ya zamo mutun na farko da ya yi balaguro zuwa can saman jannati a cikin wani jirgin fasinja da kamfaninsa ya kera.

Wani jirgin 'yan sama jannati a sararin samaniya cikin watan Afrilun 2021.
Wani jirgin 'yan sama jannati a sararin samaniya cikin watan Afrilun 2021. AFP - HANDOUT
Talla

Mista Branson ya bayyana wannan balaguron a matsayin wata kwarewa da ya cimma a rayuwarsa , yana mai fatan hakan zai bude sabon babin zuwa yawon bude ido a can saman jannati.

Jim kadan da dawowarsa doran duniya a cikin jirgin na Virgin Galactic da ya sauka  a birnin New Mexico na Amurka, Branson ya mika sakon taya murna ga daukacin tawagar da ta shafe tsawon shekaru 17 tana kera wannan jirgin.

Attajiri Richard Branson da tawagar sa cikin jirgin fasinja na Virgin Galactic da yayi bulaguro saman jannati ya dawo, ranar 11 ga watan Yuli 2021.
Attajiri Richard Branson da tawagar sa cikin jirgin fasinja na Virgin Galactic da yayi bulaguro saman jannati ya dawo, ranar 11 ga watan Yuli 2021. via REUTERS - VIRGIN GALACTIC

Jirgin ya yi tafiyar mil 53 kai tsaye kafin daga bisani ya  keta iyakar saman duniya kamar yadda hukumomin Amurka suka bayyana.

Jirgin na saman jannati, ya kwashi matuka biyu da wasu fasinjoji hudu da suka hada da shi kansa Branson.

Balaguron dai ya kasance cikin salama, yayin da jirgin ya dawo doran kasa da misalin karfe 9 da minti 40 na Safiya agogon jihohin da ke yankin tsaunuka a Amurka, wato wanda ya yi daidai da karfe 3 da minti 40 agogon GMT.

Attajirin da ya samar da jirgin Virgin Galactic Richard Branson lokacin da yayi murnar nasarar da ya samu bayan balaguro da jirgin sa ya yi saman jannati.
Attajirin da ya samar da jirgin Virgin Galactic Richard Branson lokacin da yayi murnar nasarar da ya samu bayan balaguro da jirgin sa ya yi saman jannati. Patrick T. FALLON AFP

Wannan nasarar da Branson ya samu, na nufin cewa, ya yi wa takwaransa Jeff Bezoz fintikau, wanda shi ma attajiri ne da ya yi burin zama mutun na farko da ya kafa wannan tarihin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.