Isa ga babban shafi
Rasha-Hatsarin Jirgi

An gano buraguzan jirgin saman Rasha da ya bace

Masu aikin ceto sun gano buraguzan jirgin saman fasinjan da ya yi batan-dabo a gabashin Rasha dauke da mutane 28 da suka hada da jami’an gwamnati.

Samfurin jirgin An-26 da ya yi hatsari
Samfurin jirgin An-26 da ya yi hatsari Pavel Adzhigildaev
Talla

A halin yanzu an debe tsammanin samun wani da rai daga cikin fasinjojin jirgin saman wanda ya yi batan dabo a yankin tsibirin Kamchatka da ke gabashin Rasha.

An dai dakatar da ayyukan ceto da laluben jirgin saboda shigowar duhun dare, yayin da kafofin yada labaran Rasha suka rawaito cewa, akwai yiwuwar daukacin fasinjojin sun rasa rayukansu.

Da misalin karfe 2 da minti 40 na rana ne agogon GMT, jirgin na An-26 ya bace a jiya Talata.

Gwamnan tsibirin Kamchatka mai cike da wuraren yawon bude ido da manyan dazuka, ya bayyana cewa, masu aikin ceton sun gano wani bangare na gangan jikin jirgin.

Hukumar Kula Jiragen Saman Rasha ta fitar da wata sanarwa da ke cewa, an gano buraguzan jirgin da misalin karfe 9 da minti 6 na daren Talata agogon GMT.

Bayanai na cewa, an samu katsewar layin sadarwa tsakanin jirgin da hukumomi gabanin bacewarsa, kuma daga cikin fasinjojin har da jami’an gwamnati da wani karamin yaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.