Isa ga babban shafi
Faransa

Majalisar Faransa ta amince da sabuwar dokar ta'addanci

‘Yan majalisar dokokin Faransa sun kada kuri’a da gagarumin rinjaye kan kudurin tsaurara dokokin hukunta ‘yan ta’adda, ciki har da takaita zirga-zirgar masu tsassauran ra’ayin da suka kammala zaman gidan Yari, da kuma bibiyar kafofin sadarwa jama’a don gano masu yada akidar ta tsattsauran ra’ayin.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ranar 1 ga watan Yuni shekarar 2021
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ranar 1 ga watan Yuni shekarar 2021 Bertrand Guay AFP
Talla

‘Yan majalisar dokokin na Faransa 87 ne suka kada kuri’ar amincewa da wannan kudurin na tsaurara hukunci kan ta’addancin, yayin da 10 suka hau kujerar naki, yayinda wasu 4 suka kauracewa kuri’ar ta daren jiya Laraba.

Zabin ‘yan majalisar dai ya bada damar tabbatar da matakai da dama na aiwatar da dokar ta bacin da aka kafa a kasar a matsayin na dindindin, tun bayan soma aiki da su a shekarar 2015 bayan hare-haren ta’addancin da suka yi sanadin mutuwar mutane da dama a birnin Paris.

Sabuwar dokar

Sabon sauyin ya baiwa ‘yan sandan Faransa damar takaita zirga-zirgar mutanen da suka kammala zaman dauri kan laifuka masu alaka da ta’addanci, wadanda nan bad a jimawa bad a damansu za su sake fitowa cikin al’umma a sassan kasar ta Faransa, abinda ya haifar da fargaba tsakanin hukumomin kasar.

Wannan ta sanya bada shawarar bibiyar lamurran wasu da aka taba yankewa hukunci kan laifukan ta’addanci har na tsawon shekaru 2 bayan sakinsu daga gidan Yari, kudurin da ya smau amincewar ‘yan majalisar Faransa da gagarumin rinjaye. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.