Isa ga babban shafi
Belarus-Ryanair

Dalilin da ya sa na juya akalar jirgin Ryanair-Lukashenko

Shugaban Belarus Alexander  Lukashenko ya ce, ya dauki matakin karkatar da akalar jirgin saman Ryanair ne domin kare fasinjojin da ke cikinsa kuma hakan bai saba wa doka ba a cewarsa. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ke zama a yau Laraba domin tattaunawa kan matakin  da zai dauka kan gwamnatin Belarus.

Shugaban Belarus Alexander Lukashenko
Shugaban Belarus Alexander Lukashenko Maxim Guchek Belta/AFP
Talla

Jirgin saman mai dauke da dan adawar Belarus ya yi saukar gaggawa a babban birnin Minsk bayan mahukuntan kasar sun tilasta masa bisa fargabar dana bam a cikinsa, yayin da kasashen Turai da dama suka dakatar da jigila zuwa Belarus.

Shugaban ya musanta cewa, saboda cafke dan adawar ne ya karkatar da akalar jirgin wanda ya taso daga birnin Athens na Girka zuwa birnin Vilnius na Lithuania.

Tuni kasashen duniya suka yi wa shugaba Lukashenko ca a kansa, amma ya hakikan cewa, ya juya alakar jirgin ne domin kare lafiyar mutanensa.

Shugaban wanda ke magana a gaban Majalisar Dokokin Kasar  ya kuma ce, hare-haren da ake kai wa kasarsa sun fara wuce gona da iri.

Shugaban ya yi ikirarin cewa, kasashen Ukraine da Poland da Lithuania duk sun hana jirgin na Ryanair sauka a filayensu, yana mai cewa, zabin da ya rage wa jirgin a wannan lokaci shi ne sauka a birnin Minsk.

Yanzu haka na ana dakon martanin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ga gwamnatin Belarus da zarar ya kammala zamansa da ke gudana a bayan fage a wannan Larabar.

‘Yan adawa sun bukaci Kwamitin Sulhun da ya dauki kwararan matakai kan gwamnatin Lukashenko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.