Isa ga babban shafi
Belarus

Lukashenko ya karkata akalar jirgin sama sauka a Belarus don kama dan adawarsa

Kasashen Duniya sun yi Allah wadai da matakin da gwamnatin Belarus ta dauka na tilastawa jirgin saman fasinja sauka domin kama wani dan adawa, abinda wasu kasashen ke bayyanawa a matsayin aikin ta’addanci.

Jirgin saman Boeing 737-8AS na Ryanair da kasar Belarus ta juya akalarsa sauka a kasar domin kama wani dan adawa ranar 23 ga watan Mayu 2021.
Jirgin saman Boeing 737-8AS na Ryanair da kasar Belarus ta juya akalarsa sauka a kasar domin kama wani dan adawa ranar 23 ga watan Mayu 2021. PETRAS MALUKAS AFP
Talla

 

Gidan telebijin din Belarus ya bayyana cewa, hukumomi na tsare da dan adawar Roman Protasevich mai kimanin shekaru 26 dake gudun hijira a kasar Poland bayan karkatar da jirgin da yake ciki dake kan hanyar Vilnius zuwa Minsk babban birnin kasar ta Belarus, tare da rakiyar jirgin yaki.

Martanin kasashen duniya

Wannan mataki ya haifar da mummunar suka daga kasashen Turai da kungiyar Turai da Amurka da kuma kungiyar tsaro ta NATO, kuma yana zuwa ne a daidai lokacin da shugabannin kasashen Turai yau litinin ke nazari kann takunkumin da suka kakabawa kasar Belarus.

Martanin EU

Shugabar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta shafinta na Tweeter ta bukaci gaggauta sakin dan adawar kuma dan jarida mai sukan shuga Lukashenko tare da bukatar matakin ladaftarwa ga ilahirin wadanda ke da alhakin karkata jirgin Ryanair da fasinjojin da ke ciki.

Aikin ta’addanci ne sauya akalar jirgin

Hukumar dake kula da sufurin jiragen sama ta Majalisar Dinkin Duniya tace abinda Belarus tayi ya sabawa dokokin duniya, yayin da Firaministan Poland Mateuez Morawiecki ya bayyana matakin a matsayin aikin ta’addanci da kasa ke aikatawa, yayin da Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian ya bukaci daukar matakin bai daya akan kasar.

Ita ma kasar Amurka tayi mummunar suka kan abinda ya faru, inda ta bukaci gaggauta sakin Protasevich.

Takunkumi

Yayin wani taro da zata gudanar Litinin din nan, Kungiyar Tarayyar Turai za ta tattauna kan yiwuwar kara tsaurara sabbin takunkumai kan Belarus, kan wanda ta kakaba mata a baya danagene da murkushe masu zanga-zanga da gwamnatin Shugaba Alexander Lukashenko keyi.

Tuni Lithuania da Latvia suka yi kira ga jiragen saman duniya da su kauracewa sararin samaniyar Belarus.

Gwamnati a Ireland, inda Ryanair ke da hedikwata, tace matakin "sam ba abin lamun ta ba ne.

Dalin tsare dan jaridar

A ranar Lahadi shugaban na Belarus ya bada umarnin karkatar da akalar jirgin saman fasinjojin dake dauke da daya daga cikin manyan masu adawa da gwamnatinsa Roman Protasevich, wanda aka dade ana kokarin kame shi bisa laifin shirya zanga-zangar neman tilastawa shugaba Lukashenko yin murabus a shekarar bara.

Yaudarar da shugaba Lukashenko yayi

Filin jirgin saman Minsk ya fitar da wata sanarwa tun da farko cewa jirgin dole ne ya yi saukar gaggawa a biyo bayan fargabar bam, wanda ke matsayin yaudara da shugaba Lukashanko ya shirya don tsare dan adawar da yayi kaurin suna wajen rubutu a shafukan intanet.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.