Isa ga babban shafi
Faransa - Bitaniya

Faransa ta gargadi Birtaniya kan dokokin kasuwancin Ireland ta Arewa

Kasar Faransa ta gargadi Birtaniya da kada ta kuskura ta yi wasa da dokokin kasuwancin Ireland ta Arewa da ta rattaba hannu akai a yarjejeniyar ficewar ta daga Turai.

Kasae Faransa ta gargadi Birtaniya da kada ta kuskura tayi wasa da dokokin kasuwancin Ireland ta Arewa da ta rattaba hannu akai a yarjejeniyar ficewar ta daga Turai, hoto 6 ga Maris  2021.
Kasae Faransa ta gargadi Birtaniya da kada ta kuskura tayi wasa da dokokin kasuwancin Ireland ta Arewa da ta rattaba hannu akai a yarjejeniyar ficewar ta daga Turai, hoto 6 ga Maris 2021. REUTERS - CLODAGH KILCOYNE
Talla

Ministan kula da harkokin Turai na Faransa Clement Beanue ya bayyana haka inda ya bukaci Biratniyar da ta mutunta ka’idodin da suka shafi Ireland ta Arewa wanda ya bada damar cigaba da gudanar da harkokin ta da kasashen Turai da kuma harkokin kula da kwastam duk da ficewar Birtaniyar.

Beanue yace ba zasu lamunce da duk wani yunkuri na siyasantar da lamarin ba, domin yana da matukar muhimmanci ga kasashen dake yankin baki daya.

Ministan ya bayyana yarjejeniyar kasuwancin a matsayin mai muhimmanci ga dorewar kasashen Turai, inda yake cewa ba zasu bari wata kasa tayi wasa da shi ba.

Rahotanni sun ce ana samun takun saka tsakanin kungiyoyin dake Ireland ta Arewa dangane da yarjejeniyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.