Isa ga babban shafi
Faransa - Afrika

Macron zai karbi bakwancin taron tattalin arziki na Afirka da Faransa

Faransa na Shirin karban bakwancin shugabanni da kungiyoyin yan kasar Afirka ranar 18 ga watan Mayu, kamar yadda ministan kudin kasar Bruno na Maire ya sanar ranar Lahadi.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron yayin ganawa da takwaransa na Najeriya Muhammadu Buhari a fadar gwamnati dake Abuja 3 ga watan Yuni 2018.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron yayin ganawa da takwaransa na Najeriya Muhammadu Buhari a fadar gwamnati dake Abuja 3 ga watan Yuni 2018. Présidence du Nigéria /Reuters
Talla

Le Maire yana mai cewa taron zai baiwa Faransa damar sabanta yarjejeniyoyi da dama na harkokin tattalin arziki da kasashen Afirka masamman Najeriya, tare da kokarin magance matsalolin tattalin arziki da kasashe masu tasowa ke fuskanta musamman na Afirka, bayan annobar korona.

IMF

Asusun ba da Lamuni na Duniya ya ware dala biliyan 23 don hada-hadar kudade kai tsaye ga kasashen yankin kudu da hamadar Sahara, wanda tattalin arzikinsu ya ragu da kashi 1.9% a shekarar 2020 - wanda shi ne mafi munin raguwa a tarihi.

Le Maire dake jawabi yayin ziyara a kasar Cote d’ivore, yace asusun na IMF "zai je ne kai tsaye ga tattalin arzikin kasashen Afirka don su farfado da tattalin arzikin su kuma su shiga cikin farfadowa kamar takwarorinsu na duniya.

Bruno Le Maire ya ce taron kolin zai duba hanyoyin da za a tallafawa kananan da matsakaitan kamfanonin yankin ciki har da ta hanyar lamunin bada rance. Wadannan kamfanoni sun yi gwagwarmaya wajen samun kudi a cikin yanayin koma bayan tattalin arziki, wanda ya sa aikin ya ragu da kashi 8.5% kuma ya bar kasashe 17 a nahiyar a cikin matsalar bashi a bara, a cewar IMF.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.