Isa ga babban shafi
Turai-Coronavirus

Kwararrun Turai za su gana kan matsalolin da rigakafin Korona ke haifarwa

Hukumar dake sa idanu kan ingancin magunguna a Turai ta sanar da shirinta na sake nazari kan batun daskarewar jini a jikin mutanen da aka yiwa allurar kamfanin samar da magunguna na Johnson & Johnson domin rigakafin cutar Korona.

Wata mata Mary Williams yayin karbar allurar rigakafin cutar Korona ta kamfanin AstraZeneca a birnin Newcastle dake Ingila.
Wata mata Mary Williams yayin karbar allurar rigakafin cutar Korona ta kamfanin AstraZeneca a birnin Newcastle dake Ingila. AP - Scott Heppell
Talla

Zuwa Juma’ar nan an samu bayanai har kashi 4 dangane da daskarewar jinni bayan da aka yiwa wasu allurar rigakafin cutar ta Koronaa cewar hukumar sa idanu kan magunguna ta nahiyar Turai.

Hukumar ta ce an kuma gano wasu mutanen 5 masu fama da laulayi bayan yi masu allurar rikagafin kamfanin AstraZeneca ta yadda wajen da aka tsikarawa allurar ke kumbura, sai kuma wasu jijiyoyi  dake yoyo a cikin jiki.

Wadannan batutuwa biyu na zuwa ne bayan Ikirarin da hukumar kula da ingancin magungunan ta Turai ta yi a ranar Laraba da ta gabata, inda take cewa ba safai ake samun batun daskarewar jini a jikin bil adama bayan an yiwa mutum allurar AstraZeneca ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.