Isa ga babban shafi
Italiya

Draghi ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin Firaministan Italiya

Sabon Firaministan Italiya Mario Draghi ya yi rantsuwar kama aiki a yau Asabar, a matsayinsa na shugaban gwamnati, wannan na zuwa ne bayan makonni na rashin tabbas a fannin siyasar kasar.

Mario Draghi, President of the European Central Bank (ECB), attends a news conference in Vilnius, Lithuania June 6, 2019.
Mario Draghi, President of the European Central Bank (ECB), attends a news conference in Vilnius, Lithuania June 6, 2019. REUTERS/Ints Kalnins
Talla

Draghi, wanda ya kasance tsohon shugaban babban bankin Turai ya karbi rantsuwar ne gaban shugaban kasa Sergio mattarela.

Bisa dukan alamu dai, Draghi ya hada gwamnati mai ministoci 23 da ta kumshin kusan manyan jam’iyun siyasar kasar.

Muhimman batutuwa biyu da ke gaban sabuwar gwamnatin kasar su ne yaki da cutar corona da ta hallaka mutane kusan dubu dari a kasar, sannan da tada komadar tattalin arzikin kasar da cutar ta wa mummunar illa.

A kan wannan, Draghi na bukatar cin gajiyar Yuro biliyon dari biyu, da kungiyar Tarayyar Turai ta ware don rage radadi, sai dai kungiyar ta bukaci sabuwar gwamnati ta gabatar da jadawalin kashe kudaden kafin samun wannan tallafi mai tsoka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.