Isa ga babban shafi
Wasanni

Ibrahimovic ya kafa tarihin cin kwallo 500

Zlatan Ibrahimovic ya kafa tarihi cin kwallaye 500, yayin karawar da AC Milan ta doke Croton da ci 4-0 ta kuma kasance a saman teburin gasar seria A na Italiya da maki 49.

Dan wasan AC Milan Zlatan Ibrahimovic.
Dan wasan AC Milan Zlatan Ibrahimovic. Reuters/Jake Roth
Talla

Milan ta koma baya da maki biyu a gaban abokiyar hamayyarta Inter Milan wacce ta yi sama bayan nasarar da ta doke Fiorentina da ci 2-0 a ranar Juma'a, yayin da ta baiwa Juventus dake rike da kambin gasar ta Seria A tazarar maki biyar a matsayi na uku, bayan doke Roma da ci daya mai ban haushi a ranar Asabar.

A halin yanzu adadin kwallayen da Ibrahimovic ya ci a kungiyoyin da ya haskawa da kuma kasar sa ta Sweden sun kai 501.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.