Isa ga babban shafi
AMurka-Yemen

Amurka za ta cire ‘yan tawayen Huthi daga jerin ‘yan ta’adda

Amurka ta fara kokarin cire kungiyar ‘yan tawayen Huthi ta Yemen daga jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda, lamarin da ke kawar da shamakin da kungiyoyin agaji suka ce ke kawo tarnaki ga aikin bayar da agajin gaggawa, a dadai lokacin da bangarorin da ke yaki da juna suke kaffa kaffa wajen yin na’am da tayin sulhu daga shugaba Joe Biden.

Joe Biden, shugaban Amurka.
Joe Biden, shugaban Amurka. AP Photo/Virginia Mayo
Talla

Yakin da aka shafe shekaru 6 ana yi, ya yi sanadin mutuwar duban mutane, tare da daidaita miliyoyi, kana ya haifar da abin da majalisar dinkin duniya ta kira matsalar jinkai mafi muni da aka taba gani a duniya.

A ranar Juma’a wani kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka ya ce an sanar da majalisar dattawar kasar aniyar sakataren harkokin waje, Anthony Blinken na soke matsayin ‘yan ta’adda da aka lakaba wa ‘yan tawayen Huthi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.