Isa ga babban shafi
Wasanni

Ronaldo ya sake kafa sabon tarihi a duniyar tamola

Dan wasan gaba na Juventus, Cristiano Ronaldo, a ya sake kafa wani sabon tarihi a daren Lahadi, bayan doke Sassuolo da ci 3-1 a karawar da suka yi a gasar Seria A.

Dan wasan Jeventus Cristiano Ronaldo
Dan wasan Jeventus Cristiano Ronaldo REUTERS/Massimo Pinca
Talla

Juventus ta doke Sassuolo a Allianz, saboda kwallayen da Danilo da Aaron Ramsey da Cristiano Ronaldo suka ci.

Pedro Obiang ne ya ciwa Sassuolo kwallo daya.

Kwallon da Ronaldo ya ci a wasan na jiya ya nuna cewa kyaftin din na Portugal a yanzu ya zama dan wasa daya tilo da ke cin akalla kwallaye 15 a kowacce kaka cikin shekaru 15 da suka gabata a manyan gasanni biyar na Turai, wato tun daga shekarar 2006 ya fara .

Dan wasan mai shekaru 35 na fatan jagorantar Juventus zuwa nasara a wasansu na gaba da Genoa a wasan Coppa Italia a ranar Laraba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.