Isa ga babban shafi
Amurka

Dusar kankara na barazana ga shirin raba alluran rigakafin coronavirus a Amurka

Dusar kankara mai yawan gaske da ta fara zuba da safiyar yau a yankin gabashin Amurka, ta haifar da barazana ga aikin rabawa al’ummar kasar alluran rigakafin coronavirus dake gudana.

Cinkoson ababen hawa yayin zubar dusar kanakara a garin Towson dake jihar Maryland. 16/12/2020
Cinkoson ababen hawa yayin zubar dusar kanakara a garin Towson dake jihar Maryland. 16/12/2020 Julio Cortez/AP
Talla

Tuni dai wannan dusar kankara dake lullube New York, Pennsylvania da sauran jihohin dake gabashin Amurka ta fara yawan da a yanzu tudunta ya haura kafa guda, yayinda kuma masana yanayi suka gargadi sama da mutane miliyan 60 da su kasance cikin shirin ko ta kwana la’akari da yiwuwar zubar dusar kankara ka iya zama mafi muni cikin sama da shekaru 4.

Wannan kalubale na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Amurka ta soma aiwatar da shirin rarraba alluran rigakafin cutar coronavirus, da kuma shirye-shiryen bikin Kirsimeti nan da mako daya.

A Pennsylvania ma’aikatar lura da sufurin jihar ta baiwa direbobi umarnin takaita nisan tafiye-tafiyen da suke yi, da kuma takaita gudun da suke sahararawa a baya don kiyaye aukuwar hadurra.

Zubar dusar kankarar a gabashin Amurkan dai ya tilasta soke tashin daruruwan jiragen sama, yayinda kuma makarantu da dama suka sanar da shirin rufewa, inda dalibai za su koma daukar darussa daga gida ta Intanet kamar yadda suka yi yayinda annobar coronavirus ta kai kololuwa a watannin baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.