Isa ga babban shafi
Faransa

An ci tarar hukumomin Paris saboda fifita mata

Gwamnatin Faransa ta ci tarar hukumomin birnin Paris saboda samun su da laifin karya ka’idar daukar ma’aikata, inda suka dauki mata da yawa a manyan mukaman da suka wuce kima.

Magajiyar birnin Paris Anne Hidalgo
Magajiyar birnin Paris Anne Hidalgo Ludovic MARIN / AFP
Talla

Mai rike da mukamin Magajiyar Garin Birnin Paris, Anne Hidalgo ta sanar da cewar Ma’aikatar Kula da Daukar Ma’aikata ta Kasa ta ci tarar su Euro miliyan dubu 90 ko kuma Dala dubu 110 saboda karya ka’idar daukar ma’aikatan bisa la’akari da jinsinsu.

Hidalgo ta ce an same ta da laifi ne saboda ta bai wa mata manyan mukamai 11, sabanın 5 kacal da ta bai wa maza a mukaman shugabancin birnin, abin da ke nuna cewar matan ke rike da kashi 69 na mukaman shugabancin Paris.

Jami’ar ta ce, za ta dauki kudin tarar da kanta zuwa ma’aikatar da ta ci tarar su tare da rakiyar mataimakiyarta da sauran manyan jami’an da ke aiki tare da ita, yayin da ta bayyana shi a matsayin abin takaici, rashin hankali da kuma abın da bai dace ba.

Hidalgo ta ce lokaci ya yi da mata za su ci gaba da fafutuka wajen ganin sun mamaye gurabun ayyuka sabanın maza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.