Isa ga babban shafi
Falasdinu

Babban mai shiga tsakanin Falasdinawa Saeb Erakat ya rasu

Babban mai shiga tsakani wajen sasanta rikicin Gabas ta Tsakiya daga bangaren Falasdinawa Saeb Erakat ya rasu yau Talata yana da shekaru 65 a duniya bayan ya yi fama da cutar korona.

Saëb Erakat, babban mai shiga tsakani na falasdinawa.
Saëb Erakat, babban mai shiga tsakani na falasdinawa. AP Photo/Jacquelyn Martin
Talla

Erakat wanda malami, ne kuma marubuci ya dade yana jagorancin tattaunawa tsakanin Israila da Falasdinu da zummar ganin an kulla yarjejeniyar zaman lafiya da kuma kafa kasar Falasdinu.

Daga cikin irin tarurrukan da ya halarta harda na shekarar 1991 wadda ta samar da yarjejeniyar Oslo a shekarar 1993.

An haifi Saeb Erakat ne a Birnin kudus a shekarar 1955, kuma sakamakon ganin yadda Isra’ila ta samu nasara kan kasashen Larabawa a yakin shekarar 1967 da ake yi wa lakabi da ‘Yakin Kwanaki Shida’, ya sadaukar da ransa wajen samo hanyar sasanta rikicin Gabas ta Tsakiya da kuma samarwa Falasdinawa kasa ta kansu, yayin da da idonsa, a shekaru kusan 4 da suka gabata ya ga fatar sa na kafa kasar Falasdinu na dakushewa sakamakon yadda Israila ke ci gaba da mamaye yankunan Falasdinawa da kuma goyan bayan da take samu daga gwamnatin shugaba Donald Trump.

Marigayin wanda ke cikin 'yan Majalisun Falasdinawa a shekarar 1996 na daga cikin makusanta tsohon shugaba Yaseer Arafat, kuma daga nan ya shiga cikin fitattun 'yan siyasar Falasdinawa dake jagorancin tattaunawa da Jakadun kasashen duniya.

Yana daga cikin wadanda suka halarci taron Camp David a shekara ta 2000, da kuma taron Washington a shekarar 2010 domin tattauna yadda za’a sasanta rikicin Gabas ta Tsakiyar, yayin da a shekarar 2014 ya zama Babban mai shiga tsakani a taron da shugaba Barack Obama ya shirya.

Daga bisani ya rike mukamin Sakatare Janar na kungiyar Falasdinawa PLO da kuma zama cikin manyan mashawartan shugaba Mahmud Abbas.

Erakat na daga cikin mutanen da suka fi daga muryar su wajen sukar manufofin Israila daga bangaren Falasdinawa, kuma bayan ya dade yana gwagwarmaya, ya kamu da cutar korona, kamar yadda ya sanar ranar 9 ga watan Oktoba, kafin rasuwar sa yau Talata.

A farkon rayuwar sa yayi aikin jarida da Jaridar Al-Quds a Gabashin Birnin Kudus, kuma ya mallaki digiri na farko da na biyu a bangaren siyasa daga Jami’ar San Francisco, kafin daga bisani yayi digiri na 3 a Jami’ar Bredford dake Birtaniya a kan zaman lafiya.

Erakat yayi koyarwa a Jami’ar An-Najah dake Gabar Yamma da Kogin Jordan tsakanin shekarar 1979 zuwa 1991, kuma ya rubuta tarin litattafai, daga gidansa dake Jericho.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.