Isa ga babban shafi

Messi ya sake kafa tarihi a gasar zakarun Turai

Barcelona ta soma gasar neman cin kofin zakarun  Turai da kafar dama bayan doke Ferencvarosi da ci 5 -1 a wasan na neman cin kofin zakarun Turai.

Gwarzon dan wasan duniya dake wasa a Barcelona Lionel Messi
Gwarzon dan wasan duniya dake wasa a Barcelona Lionel Messi REUTERS/Albert Gea
Talla

Kaftin din Barcelona Lionel Messi wanda ya fara zura kwallo da bugun finareti yanzu haka yana da kwallaye har 116 a wasan Champions League, amma har yanzu bai kama Ronaldo wanda ke da 130 ba (ratar 14).

To sai dai ya kafa tarihin jera wasannin kaka 16 a gasar zakarun Turai inda dole yake cin kwallo akalla guda a cikinsu.

Messin ya taya abokin karawarsa na Barcelonan Pedri mai shekaru 17 wanda ya soma kirga kwallo 1 tilo a gasar.

Fati da Coutinho da Pique da Pedri da kuma Dembela na daga cikin wadanda suka zura kwallo a wasan da Barcan tayi nasara ci 5 – 1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.