Isa ga babban shafi

An binciki gidajen Ministan lafiya da Franministan Faransa saboda badakalar korona

‘Yan sandan Faransa sun binciki gidajen mayan jami’an gwamnati da na lafiyar kasar, ciki harda Ministan Lafiya Olivier Véran da tsohon Firayim Minista Edouard Philippe, a wani bangare na binciken da gwamnati ke yi dangane da yadda aka tafiyar annobar coronavirus.

Ministan lafiyar Faransa Olivier Véran
Ministan lafiyar Faransa Olivier Véran AFP/POOL/Eliot Blondet
Talla

Ministan Lafiyar Faransa Olivier Véran na ɗaya daga cikin gomman tsoffin ministoci da na yanzu da ake bincike dangane da martaninsu kan cutar coronavirus, bayan ƙorafin da waɗanda cutar ta shafa suka gabatar.

An binciki ofishin minista Véran a matsayin wani ɓangare na binciken, kamar yadda akayiwa gidan darektan kula da lafiya ta ƙasa, Jérôme Salomon.

Masu sukar na zargin gwamnati da yin jinkiri matuka wajen soma aikin gwaje-gwaje na Covid-19 da kuma sakaci wajen baiwa sanya Kellen rufe hanci da baki mahimmanci daga farkon bullar cutar.

Wata kotu ta musamman a Faransa ne dai ta ba da umarnin gudanar da bincike kan yadda gwamnati ta tafiyar da annobar ta coronavirus.

Tuni wannan bincike ya shafi, Firayinminista Jean Castex da kuma wanda ya gabace shi, wato Edouard Philippe, kazalika wanda ta gabaci Véran a ma’aikatar lafiya, Agnès Buzyn, yayin da aka binciki gidan Sibeth Ndiaye, tsohuwar mai magana da yawun gwamnati a wannan Alhamis.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.