Isa ga babban shafi
Amurka

An aikawa Trump sakon wasika mai guba

Hukumomin Amurka sun sanar da kama wani sakon ambulan mai kunshe da gubar ‘ricin’ da aka aikewa shugaban kasar Donald Trump.

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. JIM WATSON / AFP
Talla

Kafafen yada labaran CNN da New York Times sun ruwaito cewar jami’ai a Amurkan sun samu nasarar gano sakon ne a makon da yak are, kafin ya kai ga isa fadar White House, inda akai nufin ya kai ga shugaba Trump.

Jaridar The Times dake Amurka tace sakon wasikar ya fito ne daga kasar Canada, adireshin shugaban Amurkan da jami’an bincike suka gani ne kuma ya sanya suka tantance ta, bayan kammala bincike ne kuma aka tabatar da cewar sakon na kunshe da muguwar gubar da ‘ricin’.

Yanzu haka dai hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka FBI ta kaddamar da bincike kan lamarin, tare da hadin gwiwar hukumar kula da rarraba sakwannin mail ta kasar.

Kwararru a kimiyya sun tabbatar cewa gubar ricin da ake sarrafa ta zuwa hoda ko kuma ruwa, na kassara hanyoyin numfashin dan adam, bayan haddasa masa amai da gudawa masu yawan gaske, kwanaki 3 zuwa 5 bayan shakarta, abinda ke yin sanadin rasa rai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.