Isa ga babban shafi
Girka

An fara aikin kwashe 'yanciranin sansanin Moria da wuta ta kone rumfunansu

Jami’an ‘yansandan Girka sun fara aikin kwashe ‘yan ciranin da ke sansanin bakin haure na tsibirin Moria, wadanda ke fuskantar tsananin rayuwa bayan da wuta ta kone musu matsugunai a farkon watan nan.

Wasu daga cikin 'yanciranin sansanin Moria da ke tsibirin Lesbos a Girka.
Wasu daga cikin 'yanciranin sansanin Moria da ke tsibirin Lesbos a Girka. Alkis Konstantinidis/Reuters
Talla

Gabanin fara aikin kwashe ‘yanciranin a safiyar yau Alhamis, tarin ‘yan ciranin ciki har da kananan yara na ci gaba da rayuwa kan tituna ne a tsibirin na Moria sakamakon yadda wuta ta yiwa sansaninsu barna da ya kai ga kone rumfunansu.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito cewa tun da sanyin safiyar yau ne, jami’an ‘yansandan suka isa tsibirin na Moria yayinda suka rika tashin ‘yanciranin da ke kwance bisa titunan tare da sanya su a mota don kai su wasu matsugunai na wucin gadi gabanin sake gina musu sansanin na su da wuta ta kone.

Sansanin na Moria shi ne mafi girma a nahiyar Turai da ke karbar bakin haure da masu neman mafaka a kasar ta Girka dama wadanda ke shirin shiga sauran kasashen nahiyar ta Turai.

Zuwa tsakar ranar yau Alhamis jami’an ma’aikatar kare lafiyar Al’umma ta sanar da kwashe mutane fiye da dubu 2 da 800 zuwa sabon sansanin na wucin gadi, galibinsu mata da kananan yara.

Tuni dai kungiyar likitocin kasa da kasa ta MSF ta bude cibiya a gab da sansanin don bayar da kulawar lafiya ga ‘yan ciranin musamman wadanda suka jigata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.