Isa ga babban shafi

Mai shafin Wikileaks ya gurfana gaban kotu

Magoya bayan mawallafin shafin kwarmata asirin gwamnatocin kasashe na WikiLeaks Julian Assange sun yi dandazo a farfajiyar kotun da za a fara sauraron karar dan jaridar yau Litinin a birnin London na Birtaniya.

Magoya bayan Julien Assange
Magoya bayan Julien Assange REUTERS/Peter Nicholls
Talla

Mawallafin shafin na WikiLeaks Jullian Assange mai shekaru 49 wanda ya kwarmata asirin Amurka game da yakin Iraq da Afghanistan ya isa kotun sanye da bakin kaya yau litinin, zuwansa na kotu karon farko tun bayan watan Fabarairu.

Dubunnan jama’a galibi ‘yan jaridu ne suka hallara a wajen kotun don kalubalantar yunkurin mika shi ga sauran kasashen da ke nemansa ruwa a jallo ciki har da Amurka.

Cikin kwalaye masu dauke da rubutu da masu zanga-zangar neman ‘yancin na Assange ke dagawa har da wande ke cewa, ‘‘Aikin jarida ba ta’addanci ba ne’’ yayinda wani na daban ke cewa kar ku mika Assange.

Shahararriyar mai samar da kayakin qawah ta birnin London Vivienne Westwood da ke cikin masu zanga-zangar ta yau, ta ce madatsin bayanan sirrin, ya taimaka wajen kwarmatawa duniya badakalar cin hanci da rashawa a matakai daban-daban.

Stella Moris mai dakin Assange a zantawarta ta jaridar The Times ta ce mika Assange ga mahukuntan wata kasar tamkar zartas masa da hukuncin kisa ne, yayinda ta ce ta mika kwararan hujjoji dubu 80 da ke kalubalantar mika mijin na ta wata kasa don fuskantar hukunci.

Amurka kadai na tuhumar Assange da aikata laifuka 18 ciki har da fitar da sirrika dubu 500 dangane da salon yakinta a Afghanistan da Iraqi wanda kuma matukar ya amsa laifin zai karbi hukuncin shekaru 175 a gidan yari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.