Isa ga babban shafi

EU ta gargadi Birtaniya kan mutunta yarjejeniyar fitcewarta

Kungiyar Tarayyar Turai EU ta gargadi Birtaniya kan mutunta abubuwan dake kunshe a yarjejeniyar ficewa daga kungiyar. Hakan ya biyo bayan sanarwar da Firaministan Kasar Boris Johnson ya yi cewa ko da yarjejeniya, ko babu, ala tilas kasar zata fice daga kungiyar ranar 15 ga watan gobe.

Shugabar gudanarwar Tarayyar Turai, Ursula Von der Leyen
Shugabar gudanarwar Tarayyar Turai, Ursula Von der Leyen REUTERS/Piroschka van de Wouw
Talla

Shugabar Hukumar Kungiyar Tarayyar Turai Ursula Von Der Leyen, ta ce tana sa ran Birtaniya ta aiwatar da kudirin dake kunshe cikin yarjejeniyar ficewa daga kungiyar, karkashin dokokin kasa da kasa, wanda ke matsayin abu mai muhimmanci saboda bukatar sake kulla alaka nan gaba.

Voi Der Leyen dai ta yi wannan gargadi ne bayanda Jaridar the financial times ta Kasar Birtaniya ta ruwaito firaminista Boris Johnson na shirin samar da doka da zata soke wani bangare na yarjejeniyar da aka kulla tsakanin bangarorin biyu a shekarar data gabata.

Rahoton ya ce mutane 3 dake da hannu a cikin wannan shiri na firaminista Johnson na cewa gabatar da kudirin a gaban majalisar dokoki a cikin wannan mako, zai kawo cikas ga yarjejeniyar dake da nasaba da batun shige da fice a arewacin Ireland da kuma agajin gwamnatin tsakiya ga wannan yanki.

A martanin da gwamnatin Birtaniya ta bayar ta ce tana kan yin duk mai yiwuwa wajen kawar da sauran matsaloli da suka shafi arewacin Ireland toh amma bayaga haka tana la’akari da sauran batutuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.