Isa ga babban shafi
Spain-Italy

Shirin EU na farfado da tattalin arzikin da COVID-19 ta kassara ya gamu da cikas

Kasashen Italy da Spain sun bayyana shirin neman goyon bayan kasashe 4 na kungiyar Tarayyar Turai da ke kaffa kaffa wajen fitar da kudi a kan shirin kungiyar na samar da gagarumin tallafin shawo kan radadin tattalin arziki da cutar coronavirus ta haddasa wa kasashen nahiyar Turai.

Shugabar kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen.
Shugabar kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen. Olivier Hoslet/Pool via REUTERS
Talla

Yanzu haka jagororin kungiyar Tarayyar Turai na tataunawa kan wani shirin samar da Yuro biliyan 750 don taimakawa kasashe girgije tasirin da annobar coronavirus ya yi a kan tattalin arzikinsu.

Italy da Spain na daga cikin kasashen da cutar coronavirus ta yi wa tattalin arzikinsu ta’adi amma bukatarsu ta neman gaji daga kungiyar Tarayar Turai ta gamu da turjiya daga kasashe 4 da ke tsumulmula da suka kunshi Austria Denmark Netherlands da Sweden, kuma a ana sa ran cimma matsaya kan wannan tallafi ne a taron kungiyar Turai na ranar 17 da 18 ga watan nan.

A jiya Laraba Firaministan Spain Pedro Sanchez ya shaida wa wani taron manema labarai cewa zai gana da shugabannin Netherlands da Sweden da kuma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a mako mai zuwa.

Shi ma Firaministan Italiya Giuseppe Conte ya shaida wa taron cewa zai yi tattaki zuwa Netherlands da Jamus gabanin taron na Turai.

A Laraban nan shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta bukaci kasashen kungiyar Tarayyar Turai da su hada kai, su kawar da rarrabuwar kawuna don a cimma shirin tallafin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.