Isa ga babban shafi

Za'a binciki Conte kan coronavirus

Masu Gabatar da kara a kasar Italia za su yiwa Firaminista Giuseppe Conte da ministocin cikin gida da na lafiya tambayoyi kan rawar da gwamnati ta taka wajen tinkarar annobar COVID-19 wadda ta kashe mutane sama da 34,000 a cikin kasar.

Franministan Italiya,Giuseppe Conte.
Franministan Italiya,Giuseppe Conte. REUTERS/Remo Casilli
Talla

Masu gabatar da karan daga Bergamo, birnin dake arewacin Lombardy, yankin da aka fi samun wadanda suka mutu sun kaddamar da bincike kan lamarin domin gano dalilin da ya sa gwamnati ta kasa kafa dokar takaita zirga zirga a tsakiyar watan Fabarairu.

Ana saran shugabannin su gabatar da bayanai kan rawar da suka taka wajen kare lafiyar jama’a.

A Faransa ma Babban mai gabatar da kara na kasar, yace ya kaddamar da bincike domin gano irin rawar da gwamnati ta taka wajen tinkarar annobar coronavirus wadda ta kashe mutane kusan 30,000 a kasar don gano ko jami’an gwamnati sun yi sakacin da za’a tuhume su da laifin salwantar da rayuka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.