Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya nemi soke ikon kafofin sadarwar zamani kan makomar sakwannin jama’a

Shugaban Amurka Donald Trump, ya rattaba hannu kan umarnin cirewa kafafen sadarwa na zamani a kasar ciki har da Twitter, rigar kariyar ‘yancin da suke da ita na sokewa, sakayawa, ko yin kwaskwarima ga sakwannin da aka wallafa a dandalinsu.

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. Win McNamee/Getty Images/AFP
Talla

Umarnin na Trump ya biyo bayan takaddamar da ta kunno kai tsakaninsa ta Twitter, bayanda dandalin ya sakaya sakonsa kan zanga-zangar da bakaken fata ke yi a birnin Minneapolis bisa kashe dan uwansu da wani dan sanda Derek Chauvin yayi.

Yayin kare matakin da ya dauka kan twitter, Trump yace lokaci yayi na tsawatarwa kafofin sadarwa na zamani, bayan shafe shekaru ba tare da nazari kan karfin ikon da suke da shi ba, kan makomar sakwannin mutane.

A daren ranar Alhamis ne dai kamfanin Twitter ya sakaya sakon Trump kan zanga-zangar bakaken fata a Minneapolis da wasu biranen kasar kan zargin ‘yan sanda da kashe musu dan uwa George Floyd, cikin sakon nasa Trump ya bayyana masu zanga-zangar a matsayin ‘yan daban da basu mutunta mutuwar dan uwan nasu ba, tare da cewa a shirye yake ya baiwa sojoji umarnin amfani da karfi wajen tabbatar da doka da Oda idan boren ya kazanta.

Sai dai awanni wallafar Twitter ya sakaya sakon tare da kare matakinsa da cewar, yana fifita bukatun al’umma na zaman lafiya ne sama da ra’ayin shugaban na Amurka.

Yanzu haka dai umarnin Trump na takaita karfin ikon kafafen sadarwa na zamani wajen fasalta sakwanni na gaban jami’ai masu ruwa da tsaki don nazari kan mataki na gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.