Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta kame wasu da ke shirin kai harin ta'addanci

Jami’an tsaron Faransa sun sanar da kame wasu mutane 7 da ake kyautata zaton suna shirin kaddamar da harin ta’addanci a sassan kasar bayan da aka gano shirinsu na balaguro zuwa kasashen Iraqi da Syria don mubaya’a ga shugabancin kungiyar IS.

Wasu jami'an tsaron Faransa.
Wasu jami'an tsaron Faransa. Philippe HUGUEN / AFP
Talla

Hukumar tara bayanan sirrin cikin gida a Faransa DGSI da ta kame mutanen 7 a yammacin jiya Litinin, ta bayyana mutanen a jerin wadanda aka jima ana sanya idanu kansu saboda alakarsu da kungiyoyin ta’addancin da ke yankin gabas ta tsakiya.

Wata majiyar tsaro a Faransa ta bayyanawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa yanzu mutanen 7 na shalkwatar hukumar ta DGSI, yayin da ake tsaurara bincike kafin gurfanar da su gaban Kotu.

Majiyar dai ba ta yi cikakken bayani kan shirin ‘yan ta’addan 7 ba, haka zalika ba ta fayyace yankunan da suka kitsa kai farmakin ba, sai dai ta bayyana cewa mutanen na shirye-shiryen tafiya Syria wanda ake ganin suna shirin mara baya ne a yakin da IS ke yi da kasashen duniya a Syria da Iraqi.

Tun bayan harin shekarar 2015 da ya hallaka mutane 250 a Faransar, gwamnatin kasar ke tsaurara matakan tsaro yayinda ta ke tsananta bincike kan duk wanda ake zargi da alaka da kungiyoyi ko ayyukan ta’addanci.

Gomman Faransawa ne dai suka mara baya gay akin da IS ta ke a kasashen Iraqi da Syria kafin fatattakar daularsu a bara.

Akwai dai wasu bayanai da ke nuna cewa jagorancin IS ya bukaci mambobinsa da ke Faransa su kaddamar da hare-hare kan jami’an tsaro da manyan mukarraban gwamnatin kasar, batun da ke matsayin babbar barazana ga tsaron kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.