Isa ga babban shafi
Faransa

Ma'aikatan Sufurin Faransa sun yi watsi da bukatar Macron

Al’ummar Faransa na ci gaba da fuskantar kalubalen sufuri a bukukuwan kirsimetin da ke ci gaba da wakana, dai dai lokacin ma'aikatan sufuri suka yi watsi da bukatar shugaba Emmanuel Macron da ya nemi tsagaita yajin aikin ma’aikatan sufuri a lokacin bukukuwan Kirsimeti.

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa.
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa. REUTERS/Charles Platiau
Talla

Kungiyar ma’aikatan sufurin wadanda yanzu haka suka shiga mako na 4 da fara yajin aiki, sun yi watsi da bukatar tsagaita yajin aikin don bayar da damar gudanar da bukukuwan kirsimeti cikin lumana, matakin da ya wargaza shirye-shiryen mutane da dama musamman masu shirin ziyarce-ziyarce.

Tashoshin manyan jiragen kasa masu amfani da lantarki 2 ne kadai cikin 16 ke gudanar da zirga-zirga a sassan kasar ta Faransa, bayan da ma’aikatan suka jaa daaga kan shirin shugaba Emmanuel Macron na samar da gyara a dokar fansho.

Kafin fara bukukuwan na Kirsimeti dai Shugaba Macron ya bukaci tsagaitawa da yajin aikin don tausaya daruruwan mutanen da ke shirin bulaguro, amma hadakar kungiyoyin ma’aikatan sufurin suka yi watsi da mataki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.