Isa ga babban shafi
Birtaniya

Corbyn ya nemi afuwar magoya baya kan shan kaye a zabe

Jagoran ‘yan adawa a Birtaniya Jeremy Corbyn ya nemi afuwar magoya bayansa, kan gazawar da jam’iyyar Labour ta yi, wajen kawo karshen aniyar Fira Minista Boris Johnson, ta fitar da kasar daga cikin kungiyar kasashen Turai EU a wata mai kamawa.

Jagoran 'yan adawar Birtaniya Jeremy Corbyn.
Jagoran 'yan adawar Birtaniya Jeremy Corbyn. REUTERS/Henry Nicholls
Talla

Sai dai Corbyn ya kare matsayar adawa da shirin na Brexit da suke kai, inda ya zargi kafafen yada labarai da taimakawa wajen dakile karbuwar jam’iyyar adawa ta Labour da ta shekara 100.

Kayen da jam’iyyar ta Labour ta sha a zaben Birtaniyar da ya gudana a makon jiya dai, shi ne mafi muni da ta taba gani tun kafin yakin duniya na 2.

Yanzu haka dai jam’iyyar Conservative mai mulki ke da rinjayen kashi 80 a zauren majalisar Birtaniya bayan lashe kujeru 365 cikin 650, nasara mafi girma tun bayan wadda aka gani a 1980, zamanin Margret Thatcher.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.