Isa ga babban shafi
Bolivia

Sabuwar dokar zabe a Bolivia ta haramta wa Morales yin takara

Majalisar dokokin Bolivia ta amince da wani kudirin dokar zabe da zai ba da damar gudanar da zabuka ba tare da tsohon shugaba Evo Morales ba, yayin da gwamnatin wucin – gadin kasar ke tattaunawa da masu zanga – zanga don kawo karshen tarzomar da aka shafe makonni ana yi.

Tsohon shugaban Bolivia Evo Morales
Tsohon shugaban Bolivia Evo Morales REUTERS/Carlos Jasso
Talla

Akalla mutane 32 ne suka mutu a tarzomar da ta tashi biyo bayan takaddamar da ta kunno kai kan sakamakon zaben shugaban kasar na 20 ga watan Oktoba, lamarin da ya janyo karancin abinci da man fetur a birnin La paza da sauran birane.

Dukkan majalisun biyu sun kada kuri’ar goyon baya ga kudirin da za a mika wa shugabar rikon kwarya Jeanine Anez, wacce za ta sanya hannu kai ya zama doka.

Dokar ta kuma soke sakamakon zabukan da aka gudanar ranar 20 ga watan Oktoba, sannan ta  bada damar gudanar da wasu zabukan nan gaba.

Zalika, ta haramta wa ‘yan takarar da suka yi aiki a gwamnatin da ta shude sake tsayawa takarar neman mukamin dasuka taba rikewa.

Hakan zai hana tsohon shugaba Evo Morales sake tsayawa takarar shugabancin kasar a zabe mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.