Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa na fatan cimma matsaya da Amurka dangane da haraji

Ministan kudin Faransa Bruno Le Maire ya bukaci kasashen dake kungiyar G7 da su samo hanyar warware rikicin da ya biyo bayan harajin da kasar ta sanyawa manyan kafofin sadarwar Duniya.

Kamfanonin kasashen waje da sabon harajin Faransa zai aiki a kai
Kamfanonin kasashen waje da sabon harajin Faransa zai aiki a kai Reuters
Talla

Le Maire wanda kasar sa ta batawa Amurka rai wajen amincewa da dokar da zai bata damar karbar kashi 3 na harajin da kamfanonin ke karba a cikin kasar kowacce shekara, yace taron ministocin kudaden kungiyar na iya tattauna yadda za’a warware matsalar.

Ita dai wannan sabuwar dokar da majalisa ta amince da ita a Faransa, zata shafi manyan kamfanoni irin su Google da Apple da Facebook da kuma Amazon ne mallakar Amurka, abinda ya harzuka shugaba Donald Trump yace zai mayar da martini akai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.