Isa ga babban shafi
Birtaniya

Firaministar Birtaniya ta sauka daga jagorancin jam'iyyar Conservative

A yau juma’a Firaministar Birtaniya Theresa May ta yi murabus daga mukaminta karkashin jam’iyyar Conservative, bayan da ta kasa cimma yarjejeniyar ficewar Kasar daga gungun Kasashen Turai, matakin da ya baiwa masu neman maye gurbin ta damar tsayawa takara.

Birtaniya: Theresa May ta zabi rasa mukaminta na Fira Minista sakamakon kasa ficewa daga Tarayyar Turai
Birtaniya: Theresa May ta zabi rasa mukaminta na Fira Minista sakamakon kasa ficewa daga Tarayyar Turai RFI
Talla

Duk da cewa Framinista Theresa May ta yi murabus daga kujerar ta, ba za ta sauka daga mukamin ba har sai zuwa lokacin da aka zabi wanda zai maye gurbin ta kafin karshen watan yuli mai zuwa, toh sai dai ta rasa ikon ta a kan matakin na ficewar Birtaniya daga kungiyar tarayyar turai.

Har ila yau ranar 31 ga watan oktoba mai zuwa ne ranar ficewar kasar daga kungiyar kamar yadda aka tsara, toh sai dai an samu tsaiko inda majalisar tarayyar turai ta yi watsi da shirin rabuwar daya tilo da aka mika mata.

Bayan gudanar da zaben jin ra’ayin jama’a da ya gudana a shekarar 2016, May ta hau ragamar mulki inda ta shafe tsawon shekaru 3 tana aiki tukuru wajen ganin ta cimma nasarar ficewar Birtaniya daga kungiyar, wadda a dalilin haka ta jinkirta matakin sau biyu dan cimma gaci.

Uwargida May ta sanar da murabus dinta bayan ta gaza cimma nasarar fitar da kasar daga gungun kasashen Turai.

An dai samu yan takara 11 dake neman maye gurbin ta cikin su har da Tsohon Ministan Harkokin Wajen kasar Boris Johnson, sai dai ana sa ran nan da Litinin mai zuwa, wasu su janye kafin a kai ga zaben wadanda zasu fafata da juna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.