Isa ga babban shafi
Belgium

Ana shari'ar barayin da suka sace lu'u'lu'un Euro miliyan 37

Yau Laraba za a fara shari’ar wasu gaggan barayi da suka sace lu’u'lu’un da aka kiyasta cewa kimarsa ta kai Euro miliyan 37 a filin sauka da tashin jiragen saman birnin Brussels na kasar Belgium.

Satar lu'u'lu'un da barayin suka yi a Brussles ita ce mafi girma makamanciyarta a karni na 21
Satar lu'u'lu'un da barayin suka yi a Brussles ita ce mafi girma makamanciyarta a karni na 21 livescience
Talla

Daga cikin wadanda za su gurfana a gaban kotun har da Marc Bertoldi dan asalin kasar Faransa wanda kuma shi ne ya jagoranci barayin da suka yi amfani da wasu motoci biyu a ranar 18 ga watan Fabairun 2013 domin yin kutse a filin sauka da tashin jiragen saman Brussels don tafka wannan sata.

An bayyana wannan sata a matsayin mafi girma makamanciyarta da ta faru a wannan karni na 21.

A wannan rana, Bertoldi da wasu barayi 7, na sanye ne da kakin ‘yan sanda, inda suka yi amfani da bindigogi don tilasta wa wadanda ke rakiyar mota dauke da wannan lu’u-lu’u sauke akwatunan da ke dauke da zinari da kuma lu’u-lu’u a tsakiyar filin sauka da tashin jiragen saman na Brussels.

A wancan lokaci dai, akwai wani jirgi da ke jiran wannan hajar domin jigilar ta zuwa birnin Zurich na kasar Switzerland.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.