Isa ga babban shafi
Faransa

Zanga-zangar masu rigunan dorawa ta shiga mako na 17

Dubban masu sanye da rigunan dorawa a Faransa, sun sake fita zanga-zanga a biranen kasar, don ci gaba da nuna adawa ga gwamnatin shugaba Emmanuel Macron.

Masu zanga-zangar adawa da gwamnatin shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Masu zanga-zangar adawa da gwamnatin shugaban Faransa Emmanuel Macron. AFP/Georges Gobet
Talla

Mako na 17 kenan da masu rigunan dorawa ke fita zanga-zangar a dubbansu, wadda a yanzu suka shafe sama da watanni 3 suna yi.

Zanga-zangar dai na ci gaba gudana duk da kokarin shugaba Macron na kwantar da hankula, dangane da manufofin gwamnatinsa kan tattalin arzikin kasar, inda a yanzu yake halartar dakunan taron manyan biranen kasar, domin gabatar da muhawar kan manufofin nasa, shirin da zai karkare a ranar 16 ga watan Maris da muke ciki.

Zanga-zangar adawa da shugaba Macron ta soma ne a karshen watan Nuwamban bara, a lokacin da ya bayyana matakin kara farashin mai da sauran albarkatunsa, da kuma wasu sauye-sauye da ya ce za su taimaka wajen karfafa tattalin arzikin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.