Isa ga babban shafi
Amurka

Karin 'Yan Jaridu na fuskantar barazanar kora daga White House

Shugaban Amurka Donald Trump, ya yi barazanar korar karin wasu ‘yan jaridu da ke daukar labarai a fadar White House, biyo bayan sukar matakinsa na korar wakilin kafar yada labaran CNN Jim Acosta.

Shugaban Amurka Donald Trump, yayin maida martani ga tambayoyin wakilin kafar yada labaran CNN's Jim Acosta yayin taron 'yan jaridu a Washington.
Shugaban Amurka Donald Trump, yayin maida martani ga tambayoyin wakilin kafar yada labaran CNN's Jim Acosta yayin taron 'yan jaridu a Washington. © Reuters
Talla

A ranar Larabar da ta gabata, yayin ganawa da ‘yan jaridu, Trump ya bayyana wakilin na CNN a matsayin wanda bai san aikinsa ba, a dalilin rashin jin dadin wasu tambayoyi da dan jaridar yayi kan wasu manufofin gwamnatinsa ciki har da batun ‘yan gudun hijirar dake neman shiga Amurka daga kan iyakarta da Mexico, wadanda Trump ya bayyana su a matsayin ‘yan mamaya.

Yayin da yake kare matakin korar wakilin na kafar yada labaran CNN daga fadar White House, Trump ya ce ko da tsohon shugaban kasar na jam’iyyarsa ta Republican Ronald Regan aka nemi yiwa gwamnatinsa makamanciyar wannan suka, irin matakin da zai dauka kenan.

Wannan dai shi ne takun saka na baya bayan nan da ya shiga tsakanin shugaba Trump da ‘yan jaridu, matakin da ya janyowa shugaban suka daga kungiyoyin fararen hula, wadanda ke zarginsa da rashin mutunta kafafen yada labarai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.