Isa ga babban shafi
Italiya-Turai

Kotu ta fara binciken cin zarafin bakin haure ga ministan cikin gidan kasar

Kotu a kasar Italiya ta buda soma wani binciken shara’a kan ministan cikin gidan kasar Matteo Salvini kan zargin aikata laiukan kulle jama’a, kama su ba akan ka’ida ba, da kuma amfani da karfin mulki a badakalar da ta shafi bakin hauren da aka rike a cikin jirgin ruwan Diciotti.

jirgin ruwan «Diciotti», dauke da bakin haure a gabar ruwan kasar Italiya a 21 ogusta a tashar jiragen ruwan  Catane.
jirgin ruwan «Diciotti», dauke da bakin haure a gabar ruwan kasar Italiya a 21 ogusta a tashar jiragen ruwan Catane. REUTERS/Antonio Parrinello
Talla

Nan da wani lokaci ne dai ake shirin isar da bakin haurte dake cikin jirgin ruwan na Diciotti a gaba. Inda mafi yawansu cocinan kasar ta italiya ne zasu sauke su. Bayan limaman mujami’un, sun buda kofofinsu ga bakin haureN kamar Yadda M Silvani ya sanar a lokacin wani taron siyasa da ya gudanar a arwacin kasar ta Italiya

A jiya assabar, kasar Albaniya ta bayyana amincewar karbar 20 daga cikin bakin hauren, kuma hakan yasa ta zama kasar farko a nahiyar turai da bata cikin kungiyar tarayyar turai da ta dauki irin wannan mataki

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.