Isa ga babban shafi
Faransa-Italiya

Shugaba Macron zai gana da Firaministan Italiya a Paris

A yau juma’a za a gana tsakanin shugaban Faransa Emmanuel Macron da kuma shugaban gwamnatin Italiya Giusseppe Conte a birnin Paris, ganawar da za ta gudana a cikin wani yanayi na tsamin dangantaka tsakanin kasashen biyu sakamakon bambancin ra’ayi dangane da batun karbar bakin haure.

Emmanuel Macron da Giuseppe Conte Firaministan Italiya
Emmanuel Macron da Giuseppe Conte Firaministan Italiya Ian LANGSDON / POOL / AFP
Talla

Da farko dai Firaminista Conte ya ce ba zai gana da shugaban na Faransa ba sai ya nemi gafara a hukumance, bayan da Macron ya yi kakkausar suka ga Italiya wadda ta ki amincewa wani jirgin ruwa dauke da ‘yan cirani isa gabar ruwanta, to sai dai duk da cewa Faransa ba ta nemi gafarar ba, mutanen biyu za su gana a tsakiyar ranar yau juma’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.