Isa ga babban shafi

Amurka ta sanya sunan shugaban Hamas cikin jerin na 'yan ta'adda

Amurka ta sanya sunan shugaban kungiyar Hamas ta Falasdinu Isma’il Haniya, a jerin ‘yan ta’adda tare da kakaba masa takunkumai.

Shugaban kungiyar Falasdinawa ta Hamas Ismail Haniya.
Shugaban kungiyar Falasdinawa ta Hamas Ismail Haniya. Said Khatib/AFP
Talla

Masu sharhi na kallon matakin a matsayin abinda zai sake tsananta tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya, bayan da shugaban Amurka Donald Trump, ya bayyana Kudus a matsayin babban birnin Isra’ila.

A watan Mayu na shekarar 2017, Hamas ta sanar da Haniya mai shekaru 55, a matsayin shugabanta, zalika ya kasance wanda ya jajirce wajen kalubalantar matakan Amurka a kan Falasdinu.

Sai dai sanarwar da hukumar tsaron Amurka ta fitar, ta ce Haniya nada kusanci da tsagin Sojin Hamas, wadanda kuma ke samun goyon bayansa wajen cin zarafin fararen hula.

A cewar sanarwar, Haniya na da hannu a harin ta’addanci da aka kai wa ‘yan Isra’ila, kuma Hamas ce ta kashe Amurkawa 17 a harin.

Yanzu dai Amurka ta sanya sunansa a jerin sunayen ‘yan ta’adda da kuma rufe masa kadarorin da ya ke dashi a kasar, da haramtawa duk wani dan kasar Amurka, ko kamfaninta yin mu’amala ta kasuwanci da shi.

A martanin da ta mayar wa Amurka, kungiyar Hamas ta ce matakin ba zai razanata ba, ballatana ya kai ga sauya mata manufa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.