Isa ga babban shafi
Spain

Spain ta dakatar da sammacin cafke Puigdemont

Kotun Kolin Spain ta janye sammacin cafke tsohon shugaban yankin Catalonia, Carles Puigdemont da wasu Ministocinsa hudu da suka tsere zuwa Belgium kimanin wata guda.

Tsohon shugaban yankin Catalonia Carles Puidgemont
Tsohon shugaban yankin Catalonia Carles Puidgemont REUTERS/Yves Herman
Talla

A cikin wata sanarwa da ta fitar kotun ta ce, mai shari’a Pablo Llarena da ke jagorantar shari’ar, ya yanke shawarar janye sammacin kamen ta kasa da kasa bayan wadanda ake zargin sun sanar da aniyarsu ta komawa Spain don shiga takara a zaben yankuna da za a gudanar a kasar.

Sai ai har yanzu, hukumomin Spain na da hurumin cafke Puigdemont da Ministocin da zaran sun shiga kasar kamar yadda sanarwar ta nuna.

Puigdemont ya fice daga Spain ne bayan Majalisar Dokokin Catalonia ta yi watsi da sakamakon zaben raba gardama da al’ummar yankin suka kada don neman 'yancin cin gashin kansu, lamarin da ya haddasa rashin jituwa tsakanin Puigdemont da gwamnatin tarayya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.